Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-29 10:58:19    
Ban Ki-moon ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su tsaya wuta domin Olympic

cri
Lokacin da za a bude gasar wasannin Olympic, babban sakataren MDD Mr. Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa a ran 28 ga wata cewa, yana kira ga gamayyar kasa da kasa da su tsayar da bude wuta domin Olympic,wato bangarori daban daban su daina aikace-aikacen yaki da juna.

Mr. Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ko da yake za a tsayar da bude wuta domin wasannin Olympic lokacin da aka shirya gasar wasanni ne kawai, amma zai sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa da su sake yin la'akari da barnar da yaki ke kawowa, a sa'I daya kuma zai kawo dama ga bangarorin daban daban da su yi shawarwari, kuma zai ba da taimako wajen samar da taimakon agaji ga mutanen dake yake-yake. Ya ce, tsayar da bude wuta domin Olympic, watau Olympic Truce, zai shaida cewa, idan bangarori daban daban dake cikin yaki sun iya nuna girmamawa kuma sun aiwatar da tsayar da bude wuta domin Olympic, to rikici mafi tsanani za a iya warware shi, kuma za a iya samun zaman lafiya. (Zubairu)