Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2011-10-24 14:43:50    
Matakan raya tattalin arziki da cinikayya da aka tsara a taron ministocin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a karo na hudu ya samu sahihin ci gaba

cri
Kwanan baya, Zhong Manying, shugaban sashen yammacin Asiya da Afirka na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya nuna cewa, sakamakon yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Kasashen Afirka, yanzu ana kokarin aiwatar da matakan tattalin arziki da cinikayya da aka tsara yayin taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a karo na hudu ,kuma an samu sahihin ci gaba.

A lokacin da ya ba da wani bayani a rubuce, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta aika da kugiyoyin fasaha kan aikin gona har guda 37 zuwa kasashen Afirka guda 26. Bara, kasar Sin ta horar da ma'aikata a fannoni daban daban har guda 5800 na kasashen Afirka, kana a bana, Sin tana cikin shirin kara horar da mutane fiye da 7600, bugu da kari, kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka 13 lamuni na alfarma wajen fitar da kayayyaki da darajarsu ta kai dala biliyan 4.439 ,kuma ta yafewa kasashen Afirka guda 6 bashi a fannoni 10, yawan bashin da kasar Sin ta samarwa kamfanonin kasashen Afrika matsakaita da kananan ya kai dala miliyan 67 ko fiye.

Zhong Manying ya nuna cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da matakai iri-iri kamar yadda ake fata. Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da karfafa tuntubar juna da yin hadin kai da kasashen Afirka, don gudanar da manufofi a matakai daban daban ta kan dukkan fannoni.(Maryam Yang)