Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-06-05 17:46:38    
Kiyaye tsaro a yankin Asiya da Pasifik alhaki ne da ke bisa kan kasar Sin, in ji mataimakin hafsan hafsoshin sojojin kasar Sin

cri
A gun taron da aka gudanar a ranar 5 ga wata a kasar Singapore game da tsaron Asiya, mataimakin hafsan hafsoshin rundunar sojojin kasar Sin, Ma Xiaotian ya bayyana cewa, kiyaye tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik ba ma kawai na shafar moriyar kasar Sin, haka kuma alhaki ne da ke kan kasar.

Mr.Ma ya jaddada cewa, abubuwa guda uku ne kasar Sin take kokarin neman cimmawa a yankin Asiya da tekun Pasifik, wato na farko, ta kiyaye tsaron kanta da ci gabanta, na biyu, ta kiyaye zaman lafiya da albarka a yankin Asiya da Pasifik, na uku, ta sa kaimi ga Asiya da Pasifik su bunkasa jituwa.

Mr.Ma ya yi nuni da cewa, domin cimma burin, ya zama dole kasashen shiyyar su tabbatar da sabuwar manufar tsaro ta amincewa da juna da moriyar juna da zaman daidaici da hadin kan juna, su yi kokarin kulla huldar abokantaka a tsakaninsu.

Ma ya kara da cewa, ana fuskantar kalubale ta fannin tsaron Asiya da Pasifik, duk da kwanciyar hankalin da aka samu a akasarin sassan shiyyar. A cikin irin wannan hali, kamata ya yi kasashen da abin ya shafa su tabbatar da natsuwa da hakuri, don kada a samu tsanancewar halin. Ban da wannan, a yayin da ake kara fama da matsaloli ta fuskokin teku da yanar gizo da sararin samaniya da muhallin zama, kamata ya yi kasa da kasa su kara hada gwiwa.(Lubabatu)