A ran 15 ga wata, an bude taron tattaunawa karo na farko kan batun "yin amfani da bayanai da raya birane" a gun bikin EXPO na Shanghai.
Mr. Yu Zhengsheng, sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke birnin Shanghai ya bayar da jawabi a gun bikin kaddamar da taron, inda ya ce, an mayar da "yin amfani da bayanai da raya birane" ya zama babban taken wannan taro, inda za a iya tattaunawa sosai kan yadda za a daidaita matsalolin da suke kasancewa a birane lokacin da ake kokarin raya tattalin arzikin duniya bai daya da samun ci gaban fasahohin yin amfani da bayanai.
Mr. Li Yizhong, ministan kula da masana'antu da bayanai na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara karfin samar da ayyukan yau da kullum irin na tsare-tsaren yin amfani da bayanai, kuma za ta yi kokarin yin amfani da bayanai lokacin da ake bunkasa masana'antun zamani. Kuma lokacin da ake mayar da yankuna su zama birane, za a yi amfani da fasahohin zamani da bayanai wajen mayar da masana'antun gargajiya na zamani. (Sanusi Chen)
|