Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-04-10 20:39:40    
Hu Jintao ya nuna ta'aziyya ga shugaban majalisar dokokin kasar Poland kan rasuwar shugaban kasar sakamakon hadarin jirgin sama

cri
A ranar 10 ga wata, Hu Jintao, shugaban kasar Sin, ya nuna ta'aziyya kan mutuwar Lech Kaczynski, shugaban kasar Poland, ga Bronislaw Komorowski, shugaban majalisar dokokin kasar, wanda ke kula da mulkin kasar bayan da shugaba Kaczynski ya rasu sakamakon hadarin jirgin sama.

Cikin sakon ta'aziyyar, Hu Jintao ya ce, samun labarin rasuwar Shugaba Kaczynski da masu rakiyarsa sakamakon faduwar jirgin saman da suke ciki a Smolenskaya na kasar Rasha ya sa ni bakin ciki kwarai. A madadin jama'ar kasar Sin, haka kuma da sunana, ina isar da ta'aziyya ga iyalan shugaba Kaczynski da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wajen lamarin, sa'an nan, ina nuna jejeto ga jama'ar kasar Poland.

Jirgin sama mai dauke da shugaba Kaczynski na kasar Poland ya tarwatse kasa a ranar 10 ga wata, a Smolenskaya da ke yammacin kasar Rasha, lamarin da ya haddasa mutuwar dukkan mutane 96 da ke cikin jirgin. (Bello Wang)