Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-04-10 16:05:22    
An bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Bo'ao

cri
Ranar 10 ga wata, an bude taron shekara-shekara na bana na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Bo'ao a birnin Bo'ao da ke lardin Hainan na kasar Sin, inda aka samu halartar bikin budewa Mista Xi Jinping, mataimakin shugaban kasar Sin, wanda kuma ya bayyana cewa, don cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa a nahiyar Asiya da kuma duk duniya, tare da kiyaye muhalli, kamata ya yi, kasashen Asiya su yi kokarin daidaita ayyukansu na bunkasa tattalin arziki, da raya zaman al'umma, da kuma kiyaye muhalli. Aikin da kasar Sin tana so ta yi kokarin gudanar da shi tare da hada kai da sauran kasashen Asiya.

Cikin jawabinsa, Mista Xi Jinping ya nuna cewa, ra'ayin da gwamnatin kasar Sin ta gabatar na raya kasa tare da nuna sanin ya kamata ya zo daidai da ra'ayin da gamayyar kasashen duniya suke yin kira don a bi shi na samar da bunkasuwa mai dorewa tare da kiyaye muhalli. Sa'an nan kasar Sin kullum ta kan aiwatar da ayyukanta bisa ra'ayoyin. Mista Xi ya jaddada cewa, a fannin tinkarar sauyin yanayin duniya, da karfafa iyawar kasar wajen aiwatar da aikin, gwamnatin kasar Sin ta dauki aikinta da muhimmanci, tare da nuna himma da kwazo.

Mista Xi ya kara da cewa, gwanatin kasar Sin za ta hada kai tare da sauran kasashen Asiya, don neman sauya hanyar da ake bi wajen raya kasa, da kuma cimma burin samun bunkasuwa tare da kula da muhalli. (Bello Wang)