Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-12-06 17:20:41    
Sin ta riga ta kebe kudade Yuan biliyan 6.5 domin ba da kariya ga filin ciyayi na Mongolia ta gida

cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya bayar a ran 6 ga wata, an ce, ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta kebe kudade Yuan biliyan 6.5 wajen ba da kariya ga filin ciyayi na Mongolia ta gida, ta haka yawan fadin filin ciyayin da ya samu kwararowar hamada ya ragu daga kadada miliyan 46 zuwa kadada miliyan 33.

Bayan shekara ta 2000, gwamnatin kasar Sin ta riga ta kebe kudade fiye da Yuan biliyan 1.7 wajen gudanar da aikin kyautata mummunan halin da filin ciyayi na Mongolia ta gida ke ciki. Haka kuma gwamnatin ta kebe kudade fiye da Yuan biliyan 4.7 wajen gudanar da aikin mayar da dausayi don ya zama filin ciyayi, ta yadda aka ba da kariya ga filin ciyayi na Mongolia ta gida.

An yi kiyasta cewa, ya zuwa shekara ta 2010, yawan bishiyoyin da ke filin ciyayin zai kai kashi 42 cikin kashi dari, kuma ya zuwa shekara ta 2015, wannan jimilla za ta kai kashi 48 cikin kashi dari, ta haka muhallin halittu na filin ciyayin zai fara samun kyautatuwa.(Kande Gao)