A ranar 10 ga wata, an kaddamar da taron tattaunawar masu rike da lambobin yabo na Nobel na shekara ta 2009 a nan birnin Beijing. Masu samu lambobin yabo a fannin tattalin arziki 4 ciki har da Robert A. Mundell da Daniel L McFadden sun halarci wannan taro, domin tattauna makomar tattalin arzikin duniya.
A cikin jawabin da mataimakiyar shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta Sin Chen Zhili ta yi, ta bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokari wajen tabbatar da aikin samun bunkasuwar tattalin arziki cikin hanzari, da sa himma kan aikin yin gyare-gyare ga tsarin kudi na duniya da yaki da ra'ayin ba da kariyar cinikayya.
Wakilin masu samun lambobin yabo na Nobel a fannin tattalin arziki Daniel L McFadden ya bayyana cewa, za a tattauna yunkurin sake gina tsarin tattalin arzikin duniya da nufin farfado da tattalin arziki a gun taron, kuma sabo da tattalin arzikin Sin na dogara ga aikin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, a sakamakon haka, taron tattaunawa kan aikin farfado da tattalin arziki na da babbar ma'ana ga kasar Sin.
A cikin kwanaki 3 da ake ci gaba da taron, za a kira taron tattaunawar aikin gina tsarin tattalin arziki da farfado da tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare da taron tattaunawar harkokin kudi, da taron tattaunawa tsakanin dalibai a birnin Beijing da masu rike da lambobin yabo. Mataimakin shugaban bankin duniya Lin Yifu da jami'an hukumomin kudin duniya na Sin da kwararru a duniya su ma sun halarci wannan taro .(Bako)
|