Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 09:54:30    
Yang Jiechi ya gana da ministocin harkokin waje na wasu kasashen waje

cri
A ran 9 ga wata a birnin Sharm el Sheikh dake a kasar Masar, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya gana da ministan harkokin waje na kasar Senegal Madicke Niang, da ta kasar Afirka ta kudu Maite Nkoana-mashabane, da na kasar Namibia Marco Hausiku, da na kasar Masar Aboul Gheit, da ta kasar Sierra Leone Zainab Hawa Bangura, da na kasar Chadi Moussa Faki Mahamat da suka halarci taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a karo na 4.

Wadannan ministoci sun bayyana cewa, sabbin matakai 8 da firayin ministan Sin Wen Jiabao ya sanar a bikin bude taron suna da muhimmiyar ma'ana, wadanda za su iya yin babban tasiri ga hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kana za su iya samar da moriya ga jama'ar kasashen Afirka.

Yayin da yake ganawa da Mr Niang, Yang Jiechi ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci kan dangantaka tsakaninta da kasar Senegal, kuma tana son yin kokari tare da Senegal din wajen inganta hadin gwiwarsu a fannonin aikin gona da su da kiwon lafiya da gina ayyukan yau da kullum da dai sauransu, da kara yin mu'amala kan harkokin da suka shafi bangarori daban daban.

Mr Niang ya ce, hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu yana cike da kuzari, wanda ya dace da moriyar jama'arsu. Senegal za ta tsaya tsayin daka a kan manufar Sin daya tak, kana tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da Sin kan tattalin arziki da cinikayya da kuma gina ayyukan yau da kullum.

Yayin da yake ganawa da Bangura, Yang Jiechi ya bayyana cewa, Sin tana son yin kokari tare da kasar Sierra Leone wajen inganta hadin gwiwarsu da zurfafa dangantakar abokantaka kan hadin gwiwa tsakaninsu.

Madam Bangura ta ce, an raya dangantaka tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, kasar Sierra Leone ta dora muhimmanci kan zumunci tsakaninta da kasar Sin, kana tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da Sin a fannonin gina ayyukan yau da kullum da bunkasa sha'anin makamashi da dai sauransu.

Yayin da yake ganawa da Faki, Yang Jiechi ya bayyana cewa, dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Chadi ta dace da moriyar bangarorin biyu. Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Chadi a dukkan fannoni don inganta dangantakarsu.

Mr Faki ya ce, gudummawar da Sin ta baiwa kasarsa tana da muhimmanci sosai ga jama'ar kasar, yana fatan za a kara yin hadin gwiwa tsakanin kasarsa da kasar Sin a fannonin aikin gona da ayyukan yau da kullum da makamashi da sadarwa da dai sauransu.(Zainab)