A ran 9 ga wata, a gun taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka, ministan cinikayya na kasar Sin Chen Deming ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar"dankon zumunci da zaman lafiya da hada kai da samun bunkasuwa", da yin kokari wajen karfafa yin hadin gwiwar tattalin arziki tare da kasashen Afirka, da kara ba da gudummawa ga samun bunkasuwar ayyukan gona da inganta kayan abinci da manyan ayyukan yau da kullum na kasashen Afirka.
A game da batun karfafa yin hadin gwiwa a fannonin aikin gona da manyan ayyukan yau da kullum a tsakanin Sin da kasashen Afirka, Chen Deming ya bayyana cewa, na farko, ya kamata a samu bunkasuwar aikin gona na kasashen Afirka, na biyu, ya kama a yi hadin gwiwa a fannin aikin gona a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta sabuwa hanya, na uku, ya kamata a yi kokari wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannin manyan ayyukan yau da kullum, na hudu, a kafa kyakkyawar gada ga kamfanonin Sin da na kasashen Afirka. Ya kamata bangarorin biyu su hada karfin wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannonin aikin gona da manyan ayyukan yau da kullum a tsakaninsu.(Abubakar)
|