Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 20:50:58    
Kasar Sin tana son shiga aikin tinkarar sauyawar yanayi na duniya

cri

A ran 9 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin darektan hukumar kula da aikin kasa da kasa ta ma'aikatar kudi ta kasar Sin Zhang Wencai ya furta cewa, a matsayin ta kasa mai tasowa dake son sauke nauyin dake kanta, kasar Sin tana son sauke nauyin duniya dake kanta bisa damar da take da ita wajen shiga aikin tinkarar sauyawar yanayi na duniya.

A gun taron kara wa juna sani da bankin duniya ya kira kan rahoton bunkasuwar duniya na shekarar 2010 a ranar, Zhang Wencai ya ce, babbar hanyar tinkarar sanyawar yanayi ta kasa da kasa ita ce tsarin sauyawar yanayi na MDD wato UNFCC da takardar shawara ta Kyoto, dole ne a nace ga ka'idojin da takardar shawara ta Kyoto ta gabatar musamman ma ka'idar sauke nauyi daban daban bisa karfin kasa da kasa. Ya kamata kasashe masu ci gaba su rage yawan gurbatattun abubuwa da suka fitar da su da farko, kana ya kamata su samar wa kasashe masu tasowa kudin tallafi. Ya kamata kasashe masu tasowa su yi iyakacin kokari wajen bayar da gundummawa. Ya ce, kasar Sin za ta dauki matakai masu karfi wajen sauke nauyin duniya dake kanta bisa damar da take da ita don kiyaye muhallin duniya tare da sauran kasashe.(Lami)