Ran 9 ga wata, a birnin Qingdao, an bude bikin alamar kayayyaki a karo na uku na kasar Sin, kwararru da masana ilmi na kasar Sin da na ketare, da wakilan wasu shahararrun kamfannoni da kungiyoyi fiye da 3000 sun halarci wannan biki.
Mr. Fu Shuangjian, mataimakin direkatan babbar hukumar sa ido kan tabbatar da oda a kasuwanni da masana'antu ta kasar Sin ya ce, wannan bikin alamar kayayyaki ya nuna ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin alamar kayayyaki, da kuma dandalin sana'a na kasa da kasa wajen yin musayar ilmi kan fannin alamar kayayyaki. A sa'i daya kuma, wannan biki ya aike da wani sako ga duniya, inda ya ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye ikon mallakar ilmi, tare da yin iyakacin kokarinta domin bunkasa sha'anin alamar kayayyaki. [Musa Guo]
|