A ran 9 ga wata, a birnin Nanjing, an yi bikin kammala kwas din horaswa na sojoji injiniyoyi masu aikin jin kai da gwamnatin kasar Sin ta shirya wa kasashen Afghanistan da Iraq don kawar da nakiyoyi.
Jami'ar koyon ilmin masana'antu ta rundunar soja ta kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin da ke birnin Nanjing ta shirya wannan kwas. Yawan dalibai na kasashen Afghanistan da Iraq da suka halarci kwas din ya kai 38. Bayan watanni 2 da aka yi ana horaswa, dalibai sun fahimci muhimmin ilmin kawar da bom, kuma sun kara samun fasahar kawar da bom da karfin ba da shugabanci. Bayan kammala kwas din horaswar, gwamnatin kasar Sin za ta samar da wasu na'urori masu aikin kawar da bom ga kasashen biyu.(Abubakar)
|