A ran 8 ga wata a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, firayin ministan Sin Wen Jiabao ya gana da shugabannin kasashen Uganda da Afirka ta tsakiya da Tanzania da Ruwanda da mataimakin shugaban kasar Ghana da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Gabon da suka halarci taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a karo na 4.
Shugabannin sun nuna yabo ga gwamnatin Sin da ta gabatar da sabbin matakai 8 kan hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka, sun bayyana cewa, matakan suna da muhimmiyar ma'ana ga kasashen Afirka wajen tinkarar kalubalen duniya kamar rikicin hada-hadar kudi da sauye-sauyen yanayi da kuma samun bunkasuwa mai dorewa. Sin ta gudanar da ayyuka don ba da taimako da nuna goyon baya ga Afirka, ta kasance kyakkyawar aminiya ta kasashen Afirka.
Wen Jiabao ya bayyana cewa, Sin ta yi kokari wajen kara samun hadin kai da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka, kana tana fatan yin kokari tare da kasashen Afirka wajen tabbatar da matakan hadin gwiwa a dukkan fannoni don sa kaimi ga samun bunkasuwa tare da inganta dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Zainab)
|