|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-11-09 15:31:43
|
Masanan Sin da Amurka suna yin hadin kai domin fuskantar kalubalen cutar sankara
cri
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, a ran 9 ga wata a nan birnin Beijing, za a kwashe kwanaki 2 ana taron dandalin hadin kai kan ayyukan binciken cutar sankara tsakanin Sin da Amurka na shekaru 30. Masana a fannin binciken cutar sankara kimanin 200 na kasashen Sin da Amurka sun ba da shawarwarinsu kan yadda za a tinkari cutar, kuma za su yi tattaunawa kan wasu fasahohi da kimiyyar jiyya.
Mataimakin ministan hukumar kiwon lafiya ta Sin Mr Liu Qian ya ba da kiyasin cewa, a shekarar 2020, sinawa miliyan 3 ko fiye suna iya kamuwa da cutar sankara a ko wace shekara yayin da mutane miliyan 2.5 na iya mutuwa a sakamakon cutar, saboda haka, hukumar tana fatan ba da taimakon da ya wajaba domin bunkasa ayyukan binciken da Sin da Amurka suke yi kan cutar sankara.(Amina)
|
|
|