Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 13:43:00    
Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya kammala ziyarar da ya kai kasar Masar

cri
A ran 9 ga wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya kammala ziyarar da ya kai kasar Masar ta yini 3, kuma ya bar birnin Sharm El Sheikh don komowa kasar Sin.

A ran 8 ga wata, a gun bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka Wen Jiabao ya yi jawabi, inda ya sanar da sababbin matakai 8 da Sin za ta dauka wajen sa kaimi ga samun hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, ciki har da kafa huldar abokantaka ta tinkarar sauyawar yanayi tare da kasashen Afrika da ci gaba da soke bashin da wasu kasashen Afrika suka ci da kuma ci gaba da samar da rancen kudi dalar biliyan 10 ga kasashen Afirka da rage yawan kudin harajin kwastan na kayayyakin da kasashen Afrika za su fitar da su zuwa kasar Sin, da ci gaba da kara yin hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha da aikin gona da kiwon lafiya, da kara yin mu'amala da yin hadin gwiwa a fannin ba da ilmi. Ban da haka kuma, Wen Jiabao ya gana da shugabanni fiye da 10 na kasashen Afirka da suka halarci taron, a ganin shugabannin, an samu nasara a sakamakon hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma sun bayyana cewar za su tsaya tsayin da ke kan bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, da nuna goyon baya ga moriyar kasar Sin.

A gun taron manema labaru da aka shirya kafin Wen Jiabao ya tashi zuwa kasar Sin, Wen Jiabao ya yi alkawarin cewa, a cikin yanayin matsalar kudi da duniya ke ciki, kasar Sin ba za ta rage taimakon da ta samar wa kasashen Afirka ba.

Yayin ziyarar da ya yi, firayim ministan kasar Sin ya gana da shugaban kasar Masar Muhammed Hosni Mubarak da firayim ministan kasar Ahmad Mahoud Muhammad Nazif.(Abubakar)