Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 10:43:07    
An tabbatar da dukkan matakai 8 kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a kan tattalin arziki da cinikayya

cri
A ran 8 ga wata, ministan harkokin ciniki na kasar Sin Chen Deming ya bayyana cewa a taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a karo na 4, an tabbatar da dukkan matakai 8 kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a kan tattalin arziki da cinikayya tun bayan shekara ta 2006.

Chen Deming ya gabatar da wani rahoto a wajen taron a wannan rana, inda ya bayyana cewa, a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar da aka yi a shekaru 3 da suka wuce, a madadin gwamnatin Sin, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya sanar da matakai 8 da nufin kara hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da nuna goyon baya ga bunkasuwar kasashen Afirka. A karkashin kokarin Sin da kasashen Afirka, an tabbatar da dukkan matakan 8, wannan ya alamanta cewa, sabuwar dangantakar abokantaka tsakaninsu ta shiga wani sabon lokaci.

Chen Deming ya ce, a shekaru 3 da suka gabata, yawan ciniki tsakanin Sin da kasashen Afirka a kowace shekara ya kan karu da kashi 30%. Yawan ciniki tsakaninsu a shekarar 2008 ya kai dala fiye da biliyan 100 a karo na farko. Sin ta kara zuba jari ga kasashen Afirka, yawan kamfanonin Sin dake a Afirka ya haura dubu 1. Ban da wannan, Sin ta kara ba da gudummawa ga Afirka, da shirya ba da tallafin kudi gare su, da cika alkawarin soke basussuka, da kara bude kofa ga kasuwar Afirka, da kuma gudanar da hadin gwiwarsu a fannonin zaman rayuwar jama'a da bunkasuwa.(Zainab)