Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 10:41:17    
Wen Jiabao ya gabatar da sabbin matakai 8 a taron miniscoti a karo na hudu na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri
A ran 8 ga wata a birnin Sharm El Sheikh, na Masar dake dab da teku, yayin da yake halartar taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, firaministan Sin Wen Jiabao ya yi jawabi, inda ya gabatar da sabbin matakai 8 na sa kaimi ga samun hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a duk fannoni, a sa'i daya, ya alkawarta cewa, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen Afirka kan harkokin da suka shafi kasa da kasa kamar yadda take yi a yanzu, a yunkurin kiyaye moriyar kasashen Afirka.

Firaminista Wen ya nanata cewa, gwamnatin Sin da jama'arta suna girmama ikon kai na kasashen Afirka game da 'yancin zaben tsarin zamantakewar al'umma, kuma suna nuna goyon baya ga jama'ar kasashen Afirka da su nemi hanyar da ta fi dacewa da halin wadannan kasashe. Sin ta kyautata zaton cewa, Afirka tana da karfin kawar da matsaloli ta hanyar da ta zaba da kanta.

A yunkurin sa kaimi ga samun bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka a duk fannoni bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen Afirka a halin yanzu, firaminista Wen ya ba da shawarar karfafa samun kyautatuwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu, da kiyaye moriyar bai daya, da karfafa shawarwari tsakaninsu a fannin siyasa, a yunkurin kara karfin kasashe masu tasowa na fada a ji da ikon wakilci a harkokin duniya. A sa'i daya, kamata ya yi Sin ta kara yin musayar manufofi da fasahohin tinkarar kalubalen duniya tare da kasashen Afirka, domin taimakawa musu wajen kara karfinsu na tinkarar matsaloli da samun bunkasuwa da kansu.

A ran 8 ga wata da yamma, firaminista Wen ya yi taro da manema labaru a birnin Sharm El Sheikh, inda ya amsa tambayoyin da 'yan jaridun Sin da na ketare suka yi dangane da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, da sakamako mai kyau da Sin ta samu, da tinkarar sauyawar yanayi da dai sauransu.(Fatima)