Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 10:01:42    
Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da shugabanni kasashen Afrika guda bakwai

cri
A ran 7 ga wata da dare da kuma a ran 8 ga wata da safe, a birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da shugabannin kasashen Zimbabwe, da Sudan, da Liberiya, da Comoros, da Congo Brazzaville, da kuma firayim ministocin kasashen Congo Kinshasa da na Habasha wadanda suka halarci bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da kasashen Afrika.

Wadannan shugabannin kasashen Afrika sun nuna yabo ga zumuncin gargajiya a tsakanin Sin da Afrika, kuma sun darajata sabon ci gaba da aka samu na bunkasa dangantakar a tsakanin Sin da Afrika. Suna masu ra'ayin cewa, tabbatar da matakai daban daban da aka tsara a yayin taton koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da Afrika ta kawo samun moriyar jama'ar Sin da ta kasashen Afrika, kuma ta kara samar da bunkasuwar huldar a tsakaninsu. Ban da haka kuma, shugabannin sun furta cewa, suna fatan ci gaba da yin kokarin zurfafa dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Afrika bisa manyan tsare-tsare.

Dangane da haka, firaminista Wen Jiabao ya nuna babban yabo, kuma ya ce, kamata ya yi Sin da Afrika su yi amfani da taron dandalin tattaunawa a wannan karo da kara yin hadin gwiwa don tinkarar batutuwa da kalubale na duniya kamar su matsalar kudi ta duniya da sauyin yanayi da dai sauransu, ta yadda za a tabbatar da samun bunkasuwa tare.(Asabe)