Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 09:36:42    
Kasashen Larabawa sun mai da kyakkyawan martani sosai ga jawabin firaministan Sin

cri
A ran 7 ga wata a hedkwatar kungiyar kasashen Larabawa, firaministan majalisar gudanarwa ta Sin Wen Jiabao ya yi wani muhimmin jawabi mai taken "Girmama al'adu iri daban-daban", wanda ya samu kyakkyawan martani da amincewa sosai.

Mataimakin babban sakataren kungiyar LAS Ahmad Bin Hali ya bayyana cewa, jawabin Wen Jiabao da cewa yana kunshe da muhimman batutuwa, inda ya yi kira ga bangarorin biyu da su yi kokari tare don karfafa hadin kansu, a yunkurin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwar kasa da kasa. Wannan sabon masomin hadin gwiwa ne a tsakanin kasashen Larabawa da kasar Sin.

A ran 8 ga wata, jaridar gwamnatin Masar "Al Ahram El Messai" ta gabatar da wani bayanin edita na cewa, jawabin da firaminista Wen Jiabao ya yiwa kasashen Larabawa da na musulunci, ya bayyana ra'ayin Sin na karfafa hadin gwiwa tsakaninsu cikin dogon lokaci kuma hakan yana da ma'ana.

A wannan rana kuma, kamfanin dillancin labaru na Qatar ya gabatar da bayanai kan Firaminista Wen, inda ya jaddada cewa, Sin ta dora muhimmanci kan karfafa dangantaka tsakaninta da kasashen Larabawa da na musulunci, da zurfafa kokarin amincewa da juna a fannin siyasa, da kara hadin gwiwa tsakaninsu a duk fannoni bisa manyan tsare-tsare.(Fatima)