Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 09:03:04    
Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya kawo karshen ziyarar da ya kaiwa kasar Masar

cri
A ran 8 ga wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya kammala ziyarar da ya kai kasar Masar ta yini 3, kuma ya bar birnin Sharm El Sheikh don komowa kasar Sin.

A ran nan, a gun bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka Wen Jiabao ya yi jawabi, inda ya sanar da sababbin matakai 8 da Sin za ta dauka wajen sa kaimi ga samun hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, ciki har da kafa huldar abokantaka ta tinkarar sauyawar yanayi tare da kasashen Afrika da ci gaba da soke bashin da wasu kasashen Afrika suka ci da kuma ci gaba da samar da rancen kudi dalar biliyan 10 ga kasashen Afirka. Ban da haka kuma, ya gana da shugabanni fiye da 10 na kasashen Afirka da suka halarci taron.

Yayin ziyarar tasa, Wen Jiabao ya gana da shugaba da firayim ministan kasar Masar, kuma sun samu ra'ayi daya a kan batun ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Masar. Ban da haka kuma, kasashen Sin da Masar sun kulla yarjejeniyar kara hada kai, a hedkwatar kungiyar LAS da ke a birnin Cairo, Wen Jiabao ya yi jawabi, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su nuna girmama ga al'adu duniya.(Abubakar)