Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 08:59:56    
Firaministan Sin Wen Jiabao ya yi alkawarin cewa Sin ba za ta rage ba da tallafi ga Afrika ba a yayin da ake fama da matsalar kudi ta duniya

cri
A gun taron manema labarun da aka yi a ran 8 ga wata a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, a yayin da ake fama da matsalar kudi ta duniya, Sin ba za ta rage ba da tallafi ga kasashen Afrika da kasashe masu tasowa ba, kuma ba za ta rage ba da rancen kudi gare su ba.

A gun bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da kasashen Afrika da aka yi a ran nan da safe, firaminista Wen Jiabao ya gabatar da cewa, Sin za ta samar da rancen kudi kimanin dala biliyan goma ga kasashen Afrika, kuma za ta nuna goyon baya ga hukumomin kudi na Sin da su samar da rancen kudi na musamman don raya masana'antu matsakaita da kanana na Afrika. A yayin wani taron manema labarun, firaminista Wen Jiabao ya sake nanata wannan matakin da Sin ta dauka.(Asabe)