Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 20:57:33    
Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasar Liberia wajen raya kasa

cri

Ran 7 ga wata da dare a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, firaminista Wen Jiabao na kasar Sin ya gana da Madam Ellen Johnson-Sirleaf shugaba ta kasar Liberia, inda ya nuna cewa, kasar Sin tana son ci gaba da taimakawa kasar Liberia wajen raya kasa bayan yaki.

Mr. Wen Jiabao ya ce, bayan da kasashen Sin da Liberia sun maido da huldar diplomasiyya, huldar da ke tsakaninsu ta sami ci gaba yadda ya kamata. Kasar Sin tana son ba da kwarin gwiwa ga kamfannoni masu kyau da su zuba jari a kasar Liberia, tare da gudanar da manyan ayyukan hadin gwiwa don sa kaimi ga huldar amincewar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu.

Madam Sirleaf ta nuna cewa, yanzu huldar da ke tsakanin kasashen Liberia da Sin tana da kyau sosai, taimakawar kasar Sin ta ba da gudummawa sosai ga cigaban tattalin arziki da zaman rayuwa na kasar Liberia, kuma ta moriyar jama'ar Liberia. Kasar Liberia za ta ci gaba da yin kokari domin bunkasa huldar amincewa da ke tsakanin kasashen biyu. [Musa Guo]