Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 19:20:00    
Wen Jiabao ya sanar da sabbin matakan da Sin za ta dauka kan kasashen Afrika

cri

A ran 8 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya sanar da sabbin matakai 8 da Sin za ta dauka don karfafa hadin gwiwa da kasashen Afrika a shekaru 3 masu zuwa a gun taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, ciki har da kafa huldar abokantaka ta tinkarar sauyawar yanayi tare da kasashen Afrika da ci gaba da soke bashin da wasu kasashen Afrika suka ci da kuma rage yawan kudin harajin kwastan na kayayyakin da kasashen Afrika za su fitar da su zuwa kasar Sin.

Don tinkarar batun sauyawar yanayi, kasar Sin za ta taimakawa kasashen Afrika wajen gina gine-gine 100 masu yin amfani da tsabtaccen makamashi da kara yin hadin gwiwa a fannonin dudduba yanayi ta hanyar yin amfani da tauraron dan Adam, da yin amfani da sabon makamashi da yaki da yaduwar hamada da kiyaye muhallin birane da dai sauransu.

A fannin tattalin arziki, kasar Sin za ta soke bashin da wasu kasashe mafi talauci na Afrika suka ci kafin karshen shekarar 2009, haka kuma, Sin za ta soke harajin kwastan na kayayyakin kashi 95 cikin dari da kasashe mafi rashin ci gaba na Afrika dake da huldar diplomasiyya da Sin za su fitar da su zuwa kasar Sin.(Lami)