Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 18:39:12    
Kasashen Afirka suna iya daidaita batutuwansu da kansu a cewar Wen Jiabao

cri

Ran 8 ga wata a birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar, firaminista Wen Jiabao na kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin tana gaskata cewa kasashen Afirka suna iya daidaita batutuwansu da kansu ta hanyar da suke bi.

Mr. Wen Jiabao ya yi wannan furuci ne yayin da yake yin jawabi a yayintaron ministoci a karo na 4 na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Mr. Wen Jiabao ya sake jaddada cewa, ko da yaushe gwamnati da jama'ar kasar Sin suna girmamawa ikon kasashen Afirka na zabar tsarin mulki da kansu, da kuma nuna goyon bayan jama'ar kasashen Afirka da su nemi hanyar raya kasa da ta dace da halin da kasashensu ke ciki.

Ban da haka kuma, Mr. Wen Jiabao ya yi furuci cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen Afirka kan harkokin duniya da kuma kiyaye moriyarsu.

Mr. Wen Jiabao ya yi shawarwari cewa, kasar Sin da kasashen Afirka su kara daidaita matsayinsu bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye moriyarsu tare, da kara yin shawarwari kan harkokin siyasa, da inganta ikon kasashe masu tasowa kan harkokin duniya, da kyautata tsarin siyasa da tattalin arziki na duniya. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta kara yin musayar ilmi da manufofi masu tinkarar kalubale na kasa da kasa da kasashen Afirka don taimakawa kasashen Afirka da su inganta karfinsu na tinkarar matsaloli da neman bunkasuwa da kansu. [Musa Guo]