Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-08 17:02:32    
Kasar Sin za ta karfafa aikin horar da mutane masu gwaninta na kasashe masu tasowa

cri

A ran 8 ga wata a birnin Xiamen, darektan hukumar tallafawa kasashen waje ta ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Wang Shichun ya furta cewa, a shekarun baya, gwamnatin Sin ta kara yin hadin gwiwa da kasashe masu tasowa don taimake su wajen horar da mutane masu gwaninta.

A gun bikin bude taron dandalin tattaunawa na aikin kula da teku da yankunan bakin teku tsakanin kasashe masu tasowa na shekarar 2009, Wang Shichun ya ce, gwamnatin Sin ta kara sanya muhimmanci kan yin hadin gwiwa da sauran kasashe masu tasowa a fannonin horar da mutane da musanyar ra'ayi. Bisa bukatun da wasu kasashe masu tasowa suke da su, Sin ta habaka hadin gwiwarsu zuwa fannonin tarbiyya da horar da jami'ai da kara wa juna sani da dai sauransu, wadanda suka shafi aikin gona da tattalin arziki da ciniki da tarbiyya da kiwon lafiya da sauran sana'o'i fiye da 20.(Lami)