Ran 7 ga wata a Alkahira, babban birnin kasar Masar, firaminista Wen Jiabao na kasar Sin ya gana da shugaba Mubarak, da firaminista Nazif na kasar Masar.
Yayin da yake gana da Mubarak, Mr. Wen Jiabao ya jaddada cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Masar domin dinga musayar manyan jami'ai, da zurfafa hadin gwiwa kan tattalin arziki da ciniki, da kara yin hadin gwiwa wajen tinkarar matsalar hada-hadar kudi, da sauyawar yanayi da sauran manyan batutuwa.
Mr. Mubarak ya nuna cewa, kasar Masar tana kokarin kara yin hadin gwiwa da kasar Sin. Kasar Masar tana da matsayin rinjayi a yankin Afirka, tana son taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Masar, da kasar Sin da kasashen Afirka.
Yayin da Mr. Wen Jiabao ke yin shawarwari da Mr. Nazif, takwaransa na kasar Masar, ya ce, kasar Sin tana da kwarin gwiwa kan makomar huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Kuma ya yi shawarwari guda 5 wajen ci gaba da bunkasa huldar da ke tsakaninsu.
Mr. Nazif ya ce, kasar Masar tana son zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin kan tattalin arziki da ciniki domin tinkarar matsalar hada-hadar kudi. [Musa Guo]
|