Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-07 21:24:38    
Firaministan kasar Sin ya kai ziyara hedkwatar kawancen kasashen Larabawa, inda ya yi muhimmin jawabi

cri

Firaministan kasar Sin wanda a yanzu haka yake ziyara kasar Masar Mista Wen Jiabao ya yi ziyara a hedkwatar kawancen kasashen Larabawa a ranar 7 ga wata, inda ya gabatar da wani jawabi mai lakabi "Mutunta al'adu iri daban-daban".

Mista Wen ya jaddada cewa, akwai bambanci tsakanin al'adu iri daban-daban, kowace al'ada na kunshe da ra'ayi da buri iri daya. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na mayar da Larabawa a matsayin abokan arziki da 'yan uwa. Haka kuma ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsara jerin manufofi, a kokarin nuna goyon-baya ga bunkasuwar tattalin arziki da al'adu da kyautatuwar zaman rayuwar jama'a a yankunan kananan kabilu. 'Yan kananan kabilu mabiya addinin Musulunci suna zama tare da mutanen sauran kabilu ba tare da matsala ba, wadanda dukkansu ke taimakawa ci gaba da bunkasuwar kasar Sin.

Dadin dadawa kuma, a cikin jawabinsa, Mista Wen Jiabao ya sake nanata cewa, kasar ta Sin za ta ci gaba da ingiza yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya ce, yin shawarwari cikin lumana, da kara samun fahimtar juna, da daina rikicin zubar da jini, hanya ce mafi kyau da za'a bi wajen daidaita matsalar yankin Gabas ta Tsakiya.(Murtala)