A ran 7 ga wata bisa agogon wurin, shugaba Mohammed Hosni Mubarak na kasar Masar ya gana da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao, wanda yake ziyara a kasar, bangarorin biyu sun yi musanyar ra'ayoyinsu kan bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu, da manyan batutuwan kasa da kasa da shiyya shiyya da suke mai da hankali a kai.
Mubarak ya ce, kofar Masar a bude take ga kasar Sin har abada, Masar tana maraba da abokai daga kasar Sin da su kara zuwan Masar. Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu Masar da Sin suna gudanar da hadin gwiwarsu a fannonin siyasa da tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata, ba a kasance da ko wace irin matsala.
Wen Jiabao ya ce, a yayin da yake iso kasar Masar, ya yi kamar ya dawo gidansa.(Danladi)
|