|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-11-07 16:22:19
|
|
Wen Jiabao na fatan ziyarar da yake yi a Masar za ta zama wata ziyarar yin tattaunawa da hada kai
cri
Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Masar Ahmed Mahmoud Mohamed Nazef ya yi masa, a ranar 6 ga wata da yamma, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa birnin Alkahira don yin ziyarar aiki, a lokacin ziyararsa, zai halarci bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika da za a shirya a birnin Sharm el Sheikh.
A yayin da ya gana da manema labaru, Mr. Wen Jiabao ya ce, shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 10 da kafa dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Masar. Karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, ba kawai yana dacewa da babbar moriyar bangarorin biyu ba, har ma yana da ma'ana sosai ga dangantaka tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, da kasar Sin da kasar Masar.
Kazalika kuma, Mr. Wen Jiabao ya ce, ya zuwa karshen shekarar da muke ciki, za a tabbatar da dukkan matakan hadin kai guda 8 game da taimakawa kasashen Afrika da aka gabatar a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika. A lokacin wannan taron ministoci, zai yi kokari tare da shugabannin kasashen Afrika da nufin takaita fasahohin da aka samu, da yin shirin nan gaba, domin kai sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi. (Bilkisu)
|
|
|