Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 15:51:56    
An kaddamar da taron kyautata hadin gwiwar duniya wajen kiyaye zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin tekun Aden a birnin Beijing

cri

A ran 6 ga wata a birnin Beijing, an kaddamar da taron kyautata hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen kiyaye zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin tekun Aden.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, an kaddamar da taron ne bisa bukatar rukuni na farko na kungiyar tuntubar batun 'yan fashin Somaliya na MDD, wanda ya shafe kwanaki 2 ana yinsa. A wajen taron, an yi shawarwari kan hada gwiwa wajen kiyaye zirga-zirgar jiragen ruwa a shiyya-shiyyar mashigan tekun Aden, duk a yunkurin samun hanyar tsaro mafi kyau. Rasha da Indiya da sojojin kungiyar tarayyar Turai da kungiyar tsaro ta NATO da dai sauransu sun tura wakilai domin halartar taron, wadanda kuma suke gudanar da aikin kiyaye jiragen ruwa da kansu ko kuma ta hanyar hada kai.

Yayin da yake magana da 'yan jarida, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya bayyana cewa, Sin ta nuna goyon baya ga hadin kai dake akwai tsakanin kasa da kasa wajen kiyaye zirga-zirgar jiragen ruwa. Kuma tana fatan hada gwiwa da dukkan kasashe da kungiyoyin da abin ya shafa bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD, a yunkurin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigan tekun Adan da tekun Somaliya.(Fatima)