Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 15:48:52    
Hu Jintao ya gana da shugabannin tawagogin rundunonin sojin sama na kasashe 30

cri

A ran 6 ga wata da safe a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin sojoji na tsakiyar na kasar Hu Jintao ya gana da shugabannin tawagogin rundunonin sojin sama na kasashe 30 wadanda suka zo nan birnin Beijing bisa gayyatar da aka yi don halartar dandalin tattaunawa na duniya kan zaman lafiya da bunkasuwa a yayin cika shekaru 60 da kafa rundunar sojojin sama ta 'yantar da jama'ar kasar Sin. Hu Jintao ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da yin tsayin daka kan tunanin zaman lafiya da bunkasuwa da kuma hadin gwiwa, da raya ayyukan sufurin sama cikin lumana, da hada gwiwa tare da kasa da kasa a fannin samar da tsaron sama don inganta sararin samaniya ta yadda za a iya samun damar cin moriyar juna, da kuma inganta sha'anin samun zaman lafiya da bunkasuwa na dan Adam.

Hu Jintao ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da kokarin raya kasa cikin lumana, da hada gwiwa tare da dukkan kasashe a karkashin ka'idoji 5 na zaman tare cikin lumana, da yin kokari wajen kafa wata duniya mai zaman lafiya da wadata. Sin za ta ci gaba da yin tsayin daka kan manufofin tsaron kasa, kuma ba za ta habaka ayyukan soja da yin gasar jan damara ba har abada, kana ba za ta yi barazana ga sauran kasashe a fannin aikin soja ba.(Zainab)