Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 15:48:24    
An nuna hotuna kimanin dari biyu kan kyakyawan gani na Afrika

cri

A ran 6 ga wata, a birnin Beijing, an nuna hotuna kimanin dari biyu da masu dauka hotuna guda 9 suka dauka a Afrika.

Jigon wadannan hotuna ya shafi mazauna Afrika, da al'adun kasashen Afrika, da kuma bunkasuwar kasashen Afrika, kana da zumuncin dake tsakanin Sin da Afrika da dai sauransu. Za a ci gaba da wannan bikin nuni har zuwa ran 15 ga wata.

Yayin da ta halarci bikin bude bikin nune-nune, mataimakiyar shugabar hukumar kula da harkokin waje ta ma'aikatar al'adu ta kasar Sin Li Hong ta bayyana cewa, ma'aikatar ta yi shirin cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa, masu dauka hotuna na kasar Sin za su ziyarci dukkan kasashen Afrika, ta yadda jama'ar kasar za su fi fahimtar Afrika daga dukkan fannoni.

A gun bikin, mashawarci kan al'ada na ofishin jakadanci na kasar Senagal dake kasar Sin Mbacke Ndiaye Saye ya furta cewa, masu daukar hotuna na kasar Sin sun nuna hakikanin zaman rayuwar Afrika cikin zumunci da adalci.(Asabe)