|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-11-06 14:40:51
|
An yi bikin jana'izar Qian Xuesen
cri
Wakilimu ya ruwaito mana labarin dake cewa, a ran 6 ga wata, an yi bikin jana'izar Qian Xuesen, wani masani a fannin kimiyya a makabartar jama'a ta Ba Baoshan dake Beijing. Shugabannin kasar Sin da dama kamar shugaba Hu Jintao sun halartar bikin.
An haifi Mr Qian Xuesen a shekarar 1911 a birnin Shanghai, ya taba yi karatu a Amurka, a lokacin yana da shekaru 28 a duniya, ya zama wani mashahurin masani a duniya. A shekarar 1955, ya komo kasar Sin, kuma ya taka muhimmiyar rawa kan sha'anin kimiyya da fasaha da tsaron kasa da kuma sha'anin sojoji na zamani, saboda haka, ana kiransa " Mutumin da ya aza harsashi ga sashin nazarin ilimin zirga-zirga a sararin samaniya" da kuma "Sarkin roka". A ran 31 ga watan Octoba na bana a nan birinin Beijing, Mr Qian Xuesen ya rasu yana da shekaru 98 a duniya.(Amina)
|
|
|