Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 09:57:42    
Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya tashi don kai ziyarar aiki a kasar Masar da halartar sabon taro na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da Afrika

cri
A ran 6 ga wata da safe, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasar Masar. A cikin kwanaki uku masu zuwa, Wen Jiabao zai kai ziyarar aiki a kasar, kuma zai halarci bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da Afrika da za a yi a Sharm el Sheikh.

Bisa labarin da ma'aikatar harkokin waje ta fayyace, an ce, a yayin ziyarar da zai yi a bisa gayyatar da takwaransa na Masar Ahmed Mahmoud Mohamed Nazef ya yi masa, Wen Jiabao zai gana da shugaban kasar Masar Muhammed Hosni Mubarak da firaministan kasar Ahmed Mahmoud Mohamed Nazef, kuma bangarorin biyu za su sa hannu kan takardun hadin gwiwa. A gun bikin bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da Afrika, Wen Jiabao zai ci gaba da gabatar da sabbin matakai a jere na kara karfin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika. Ban da haka kuma, Framinista Wen zai ziyarci hedkwatar kungiyar tarayyar kasashen Larabawa dake birnin Alkahira, inda zai gana da babban sakataren kungiyar don kara hadin gwiwa mai kawo moriyar juna a tsakanin Sin da kasashen Larabawa.

Ziyarar Mista Wen Jiabao a wannan karo ta zo daidai lokacin ranar cika shekaru goma ta kafuwar dangantakar hadin kan Sin da Masar bisa manyan tsare-tsare. Kuma wannan ziyara ita ce karo na farko da firaministan Sin ya ziyarci hedkwatar kungiyar tarayyar kasashen Larabawa bayan da Sin da kungiyar suka bayar da sanarwar kafa dangantakar abokantaka ta sabon salo mai shimfida zaman lafiya da samun dauwamamman ci gaba a tsakanin Sin da kasashen Larabawa.(Asabe)