Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 20:34:21    
Za a shirya taron neman hadin kai da samun sulhuntawa kan aikin ba da kariya a tekun Aden

cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Ma Zhaoxu ya bayyana a ran 5 ga wata a birnin Beijing cewa, bisa bukatar kungiyar aiki ta farko ta hukumar sadarwa kan matsalar 'yan fashi a tekun Aden ta MDD, ma'aikatar tsaro ta kasar Sin za ta shirya taron neman hadin kai da samun sulhuntawa kan aikin ba da kariya a tekun Aden daga ranar 6 zuwa 7 ga wata.

Mr. Ma ya yi wannan bayani ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a ran nan, inda ya ce, a gun taron za a tattauna batun hadin kai da ke tsakanin kasa da kasa domin su ba da kariya a yankunansu daban daban a tekun Aden, ta yadda za a iya gudanar da aikin ba da kariya mai inganci cikin hadin gwiwar kasa da kasa. Mr. Ma ya ci gaba da cewa, har kullum kasar Sin tana daukar matsayin bude kofa ga samun hadin kai a tsakanin kasa da kasa kan aikin ba da kariya a teku, kasar Sin tana son yin hadin kai da kasashen da abin ya shafa ta hanyoyi daban daban kuma bisa kudurin kwamitin sulhu na MDD, domin kiyaye zaman lafiya a mahadar ruwan tekun Aden.(Danladi)