Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 14:39:19    
An kaddamar da aikin daukar sabbin sojoji a lokacin sanyi a kasar Sin

cri

A kwanakin baya, an kaddamar da aikin daukar sabbin shiga da rundunar sojar 'yantar da jama'ar kasar Sin a lokacin sanyi na shekarar 2009, kuma daliban jami'o'i suna da himmar shiga aikin sojojin. Ban da wannan, Sin ta gabatar da manufofi masu tarin yawa wajen jawo daliban jami'o'i su shiga aikin sojoji don tsaron kasa.

An fara daukar sabbin sojoji daga daliban jami'o'i da suka kammala karatu a bana, wannan aiki ya bambamta da na da. Bisa kididdigar da hukumomin ba da ilmi na kasar suka gabatar, an ce, yawan daliban da suka yi rajista don shiga aikin sojoji ya kai dubu 130, wanda hakan ya dara na shekarun da suka gabata. Za a gudanar da manufofin da zai kyautata wa daliban da suka shiga sojoji a bana, ciki har da ba da kudin rangwame a jami'a, da samar musu da aikin yi bayan sun bar aikin sojoji da dai sauransu. Bayan sun shiga aikin sojoji, kowanensu zai iya samu kudin rangwame Yuan dubu 24.(Zainab)