Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 14:33:47    
Kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya yi hadin gwiwa tare da kafofin watsa labaru na duniya don watsa labaru game da ranar yara ta duniya

cri

A ran 5 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya rattaba hannu kan yarjejeniya tare da asusun yara na M.D.D, inda suka samu ra'ayi bai daya da cewar kafofin yada labarai na kasashe da yankunan duniya za su shirya ayyukan taimakon jama'a da yada labarai cikin hadin gwiwa a fadin duniya game da kare hakkin yara a ran 20 ga wata domin murnar cika shekaru 20 da kaddamar da yarjejeniyar kiyaye hakkin yara.

Wannan ne karo na farko da kafofin watsa labaru na duniya za su yi ayyukan ba da taimako da yada labarai kan batu daya da lokaci daya. Bisa labarin da aka bayar, an ce, ya zuwa ran 4 ga wata, yawan kafofin watsa labaru na kasa da kasa da suka yarda da shiga wannan aiki ya wuce 500.A ran 20 ga wata, tun daga karfe 8 na safe, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin zai yi hadin gwiwa tare da kafofin watsa labaru da abin ya shafa wajen watsa labaru a cikin awoyi 24 a nahiyoyi 6 na duniya.(Abubakar)