Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 20:23:07    
"Aikin kiyaye hakkin dan Adam a kasar Sin na samun bunkasuwa sosai", in ji babban direktan ofishin kula da harkokin yada labaru na majalisar gudanarwa ta Sin

cri
A ranar 4 ga wata, jaridar People's daily ta buga bayanin da babban direktan ofishin kula da harkokin yada labaru na majalisar gudanarwa ta Sin Wang Chen ya yi, inda ya bayyana cewa, dangane da aikin zamanintar da kasar Sin da samun bunkasuwa a cikin shekaru 60 da suka gabata, aikin kiyaye hakkin dan Adam a kasar Sin na cigaba da samun bunkasuwa sosai.

Hakan ya ce, a cikin shekaru 60 da suka gabata, zaman rayuwar al'umma a kasar Sin na samun bunkasuwa daga zaman talauci zuwa zaman wadata. Game da rikicin kudin da duniya ke ciki, Sin ta gabatar da matakai da dama wajen kara yawan bukatun sayayya a gida da kyautata zaman rayuwar al'umma, domin kiyaye hakkin dan Adam.

A gefe daya kuma, ikon kula da al'umma da siyasa da jama'a na cigaba da samun bunkasuwa sosai. Zaman rayuwar jama'a iri na demokuradiyya na cigaba da samun bunkasuwa, a cikin watan Afrilu, hakazalika gwamnatin Sin ta tsara shirin kiyaye hakkin dan Adam na kasar, kuma an tsara shirin samun bunkasuwar aikin kiyaye hakkin dan Adam daga dukkan fannoni a cikin shekaru 2 masu zuwa.

Bayanin ya ce, Sin ta dukufa ka'in da na'in wajen hada gwiwa da kasashen duniya da sa kaimi ga samun bunkasuwar sha'anin kiyaye hakkin dan Adam a duniya. Akwai kalubaloli da wahalhalu da dama da Sin za ta fuskanta wajen sa kaimi da tabbatar da hakkin dan Adam.(Bako)