Bankin duniya ya gabatar da sabon rahoto kan kasar Sin na duk bayan watanni uku a ran 4 ga wata, inda ya bayyana cewa, a karkashin shirin sa kaimi ga tattalin arziki, tattalin arzikin Sin zai karu da kashi 8.4% a bana.
Rahoton ya nuna cewa, a sakamakon rashin bukatun waje da raguwar kayayyakin da ake fitar zuwa kasashen waje, saurin karuwar tattalin arzikin Sin a watanni 9 na farkon bana ya ragu da kashi 3.6%. Amma a sakamakon aikin zuba jari bisa jagorancin gwamnatin kasar, an maido da saye-saye da zuba jari a kasar, karuwar bukatun cikin gida ta sa kaimi ga karuwar fitar da kayayyaki.
Kazalika rahoton ya ce, ko da yake farashin wasu abinci ya karu a yanzu, amma ta la'akari da halin tattalin arzikin duniya da na Sin, ba a samu hauhawar farashin kaya a kasar Sin a yanzu ba.
An kimanta halin da tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2010 ke ciki a cikin rahoton, inda aka ce, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da karuwa a shekarar 2010, saurin karuwarsa zai kai kashi 8.7%.(Zainab)
|