Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 10:15:35    
Mutanen kasar Sin da ke da shirin yawon shakatawa a kasashen waje sun mayar da hankali kan nahiyar Afirka

cri

Taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a karo na 4 ya sa nahiyar Afirka ta jawo hankulan jama'a, 'yan kasar Sin da ke da shirin yawon shakatawa sun mai da hankali kan nahiyar Afirka.

Bisa labarin da wasu kamfannonin yawon shakatawa na birnin Beijing suka bayar, an ce, tun daga watan Oktoba, an kara samun buga waya da ake yi don neman bayanan yawon shakatawa a Afirka da kashi 30% zuwa 50% bisa na makamancin lokacin bara, an kara tura tawagogin yawon shakatawa zuwa Afirka, yawan masu yawon shakatawa da suke zuwa Afirka a kowane wata ya kai dari 2 zuwa dari 3.

A yanzu dai, kasashe 17 na Afirka sun zama kasashen da 'yan kasar Sin suke iya yawon shakatawa.

A ganin masana a wannan fanni, ko da yake yawan mutanen Sin da suke zuwa Afirka don yin yawon shakatawa ya kara karuwa, amma yawansa bai taka kara ya karya ba. Sabo da haka, sha'anin yawon shakatawa na Afirka yana da kyakkyawar makoma. Kana gasar kwallon kafa ta duniya da za a gudanar a kasar Afirka ta kudu a badi za ta jawo dama wajen bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa na Afirka.(Zainab)