Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 08:58:31    
Kamata ya yi Sin ta samu bunkasuwa mai dorewa bisa kimiyya da fasaha, in ji firaminista Wen Jiabao

cri

A ran 3 ga wata, yayin da yake yin jawabi ga sashin kimiyya da fasaha na birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, firaminista Wen Jiabao ya nuna cewa, kamata ya yi Sin ta samu bunkasuwa mai dorewa bisa kimiyya da fasaha.

Wen Jiabao ya bayyana cewa, zamanintar da kasar Sin wani babban sauyi ne da ba a taba ganinta a tarihin dan Adam ba. Kimiyya da fasaha muhimmin karfi ne wajen sa kaimi ga samun wannan sauyi. A sabili da haka, dole ne Sin ta dogara da kimiyya da fasaha wajen raya kanta da kuma kawowa jama'a sama da biliyan daya alheri. Kuma dole ne Sin ta kammala aikin zamanintar da kanta irin ta demokuradiyya mai albarka cikin lumana tun da wuri bisa kimiyya da fasaha.

Bayan haka, Wen Jiabao ya jaddada cewa, idan kasar Sin tana so ta sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa a duk fannoni cikin dogon lokaci, kuma ta rika samar da sabbin kayayyaki da kara biyan bukatun jama'a cikin gida, to, dole ne ta mayar da kafa wata kasa mai samar da sabbin kayayyaki a matsayin burinta bisa manyan tsare tsare, da daukar samun bunkasuwa mai dorewa a matsayin hanyarta, da kuma daukar samun bunkasuwar tattalin arziki da kimiyya da fasaha a matsayin muhimmin aikinsa, ta yadda za ta mayar da sabbin sana'o'i a matsayin babban karfin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma bisa manyan tsare-tsare.(Fatima)