Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 16:30:12    
Yawan makamashi mai bola jari da za a yi amfani da su a kasar Sin zai kai kashi 10 cikin dari na yawan makamashi da za a yi amfani da su a kasar a shekarar 2010

cri
Bisa labarin da jaridar People's Daily ta bayar, an ce, wani jami'in kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar 2010, yawan makamashi mai bola jari da za a yi amfani da su a kasar Sin zai kai kashi 10 cikin dari na yawan makamashi da za a yi amfani da su a kasar. Duk da kasancewar wahalhalun da za a fuskanta don cimma wannan buri, amma ba a nuna damuwa ba.

A ran 2 ga wata, a gun taron koli game da makamashin da ba za su gurbata muhalli na duniya wanda aka yi a kasar Sin, mataimakin shugaban cibiyar nazarin makamashi na kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Li Junfeng ya gabatar da cewa, a cikin wadannan makamashi mai bola jari, yawancinsu su ne karfin ruwa da iska da aka yi amfani da su don samar da lantarki, da kuma zafin rana da dai sauransu. Bugu da kari, Li Junfeng ya ce, fadin katakon tara zafin rana don samar da ruwan dumi ya kai muraba'in mita miliyan 150 a kasar Sin, hakan yana daidai da cewa, yawan kwal da aka yi amfani da su ya ragu da ton miliyan goma ko fiye. Ban da haka kuma, a kasar Sin, da akwai gidaje kimanin miliyan 30 da suke yin amfani da irin gas da ake samu daga bola, wannan adabi ya yi yawa sosai.(Asabe)