Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 15:36:43    
Kasar Seychelles ta ba da kyautar kunkuru guda 2 irin na Aldabra Giant ga bikin baje koli na duniya a birnin Shanghai

cri

A ran 2 ga wata da yamma, a gidan zu na birnin Shanghai, an gudanar da bikin ba da kyautar kunkuru guda 2 irin na Aldabra Giant ga bikin baje koli na duniya a birnin Shanghai, wadanda suka fi girma a duniya, kuma shekarunsu za su kai 250 da haihuwa. A sabili da haka, suna da daraja kwarai.

Jakadan Seychelles a Sin, kana babban wakilin kasar Seychelles Philippe Le Gall ya bayyana cewa, kasar jamhuriyyar Seychelles na daya daga cikin kasashen duniya da tuni suka yanke shawarar shiga wannan bikin baje koli. Tana iyakacin kokarinta domin nuna goyon baya ga aikin share fagen bikin baje koli na kasa da kasa a birnin Shanghai. A lokacin cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin, Seychelles ta ba da kyautar kunkuru 2 irin na Aldabra Giant ga gwamnatin birnin Shanghai da bikin baje koli, a yunkurin bayyana zumunta mai zurfi tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a yunkurin kara fahimtar da jama'ar Sin ga wadannan wakilan sada zumunta, daga ran daya ga watan Disamba na bana zuwa ran 30 ga watan Afrilu na badi, gidan zu na birnin Shanghai zai gudanar da gasar neman sunayen kunkuru biyu bisa jagorancin hukumar kyautata harkokin bikin baje koli na kasa da kasa a birnin Shanghai da hukumar kula da tsire-tsire ta birnin Shanghai. A ran 18 ga watan Yuni na shekarar 2010, wato ranar kasar Seychelles wajen bikin baje koli na kasa da kasa a birnin Shanghai, wanda ya ci wannan gasa zai samu wani kwa-kwa, wanda ya tsiro a Seychelles, 'ya'ya ne na wani itacen tafin hannu mai al'ajabi.(Fatima)