Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 09:37:48    
Ministan kiwon lafiya na kasar Sin ya bukaci wurare daban daban da su dauki tsauraran mataki don sassauta yaduwar annobar cutar A(H1N1)

cri
A ran 2 ga wata, a gun taro game da ayyukan da duk hukumomin kiwon lafiya na kasar Sin suka yi na rigakafi da yaki da cutar A(H1N1), ministan kiwon lafiya na kasar Sin Chen Zhu ya bukaci hukumomin kiwon lafiya na wurare daban daban da su dauki tsauraran mataki don sassauta yaduwar annobar cutar, da rage mutanen da za su kamu da cuta mafi tsanani ko za su mutu sakamakon cutar.

A gun taron, mista Chen Zhu ya ce, kasar Sin ta riga ta shiga lokacin da annobar cutar ta fi yaduwa, kuma yawan mutanen da suka kamu da cutar ya karu da sauri. Yawan mutanen da za su kamu da cutar da karfin yaduwar cutar za su zarce shekaru da suka gabata. Kuma lokacin yaduwar annobar a wannan karo zai ci gaba da zuwa watan Maris na shekara mai zuwa. Amma ana sa ran cewa, watakila kwayoyin cutar ba za su canja ba.

Bugu da kari, mista Chen Zhu ya yi nuni da cewa, ya kamata hukumomi na wurare daban daban su kara karfin yin jagora da ba da taimako ga aikin rigakafi da yaki da cutar a makarantu, kuma kamata ya yi su dauki matakin yin rigakafi da yaki da cutar a makarantun da annobar cutar ta abku, kana su dauki matakin daina karatu da dai sauransu a lokacin da ake bukata. Ban da haka kuma, kamata ya yi hukumomin kiwon lafiya na wurare daban daban su yi kokari da hukumomin yada labaru, ta yadda za a yada labaru game da annobar cutar da ayyukan rigakafin cutar cikin lokaci kuma a fili.(Asabe)