Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 22:05:34    
Minista mai kula da harkokin musamman na kasar Nijeriya ya yi kira da a ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika

cri

A ranar 2 ga wata, a nan birnin Beijing, yayin da minista mai kula da harkokin musamman na kasar Nijeriya Ibrahim Musa Kazaure ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, kasashen Afrika na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin.

Ibrahim Musa Kazaure ya fadi haka ne yayin da ya tabo maganar taron ministoci a karo na 4 na dandanlin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika da za a yi a birnin Sharm El Sheik da ke kasar Masar. Ya bayyana cewa, shugabannin kasar Sin da na kasashen Afrika za su zauna tare, domin tattauna matsalolin da ke damun kasashen Afrika. Shugabannin kasashen Afrika za su bayyana ra'ayoyinsu a gun taron, a yunkurin kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu.

A yayin ganawar, ministan ya ce, zai sa ido sosai kan taron dandanlin tattaunawar da za a yi a kasar Masar, kuma yana fatan kasar Sin da kasashen Afrika za su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu.

Bisa goron gayyatar da taron nazarin kiyaye hakkin bil Adama na Sin ya yi, Minista Ibrahim Musa Kazaure ya zo kasar Sin domin halartar taron dandalin tattaunawar kiyaye hakkin bil Adama a karo na 2 da aka yi a nan birnin Beijing, ya bayyana cewa, taron dandalin tattaunawar ya sa shi kara fahimtar halin da ake ciki wajen kare hakkin bil Adama a kasar Sin, yana ganin cewa, wannan taro ya daukaka ingancin Sin wajen taka rawar a zo a gani a fannin kiyaye hakkin bil Adama a dukkan kasashen duniya.(Bako)