Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 21:59:20    
Kasashe da shiyyoyi da yawansu ya kai 122 za su halarci taron tattaunawar hadin gwiwa kan zuba jari a ketare a karo na farko a nan kasar Sin

cri
Daga ranar 3 zuwa 4 ga wata a nan birnin Beijing, za a shirya taron tattaunawar hadin gwiwa kan zuba jari a ketare na kasar Sin. Ya zuwa yanzu, kasashe da shiyyoyi, wadanda yawansu ya kai 122 sun tabbatar da halartar taron, ciki har da kasashe mafiya karancin ci gaba 50 a duniya da M.D.D. ta tabbata.

An samu labari daga taron manema labaru da aka shirya a ranar 2 ga wata cewa, a gun taron, kasashen ketare za su yi nune-nune a fannonin makamashin ma'adinai, da manyan ayyuka, da sana'ar sadarwa, da sabbin makamashi, da dai sauransu, yawansu zai wuce 2000. A yayin taron kuma, kasashe da shiyyoyi fiye da goma za su shirya tarurruka, don yin bayani kan zuba jari, da kuma dandalin tattaunawa, inda za su bayyana yanayin zuba jari da kasashensu ke ciki, da kuma ba da taimako ga hadin gwiwa tsakanin masana'antun kasashensu da na kasar Sin. (Bilkisu)