Ministan aikin gona na kasar Sin Mr. Sun Zhengcai ya bayyana a kwanakin baya cewa, daga shekarar 2006 kasar Sin ba za ta karbi kyautar hatsi daga hukumar kula da shirin abinci ta MDD, daga lokacin kuma sannu a hankali kasar Sin ta zama wata muhimmiyar kasa da take ba da kyautar hatsi ga kasashen da suke bukata.
A halin yanzu yawan hatsi da kasar Sin ta samu ya kai matsayi na farko a duk duniya. Minista Sun ya kyautata zaton cewa, yawan hatsi da kasar Sin za ta samu a shekarar da muke ciki zai kai wani sabon matsayin koli, wato zai karu a cikin shekaru 6 a jere a karo na farko kusan shekaru 40 da suka gabata.
Mataimakiyar darekta ta hukumar kula da shirin abinci ta MDD Madam Sheila Sisulu ta bayyan a 'yan kwanakin baya cewa, a halin yanzu kasar Sin ba kawai ta ba da kyautar hatsi ga kasashen da suke bukata ba, har ma ta iya zama wani dakin gwaje-gwaje da kasa da kasa suke gudanar da nazari kan samarwa da inganta hatsi.(Danladi)
|