Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 15:28:16    
Yawan kudin cinikayya a tsakanin Sin da Afrika ya kai dala biliyan 100

cri
A ran 2 ga wata, a birnin Beijing, mataimakin ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin Chen Jian ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an tabbatar da matakai takwas na hadin kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afrika wadanda aka gabatar a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika a shekarar 2006. Yawan kudin cinikayya a tsakanin Sin da Afrika ya kai dala biliyan 100, abin da ya ba da damar cimma buri kafin shekaru biyu da aka shirya.

Daya daga cikin muhimman ayyukan da za a yi a gun taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika shi ne kimanta ayyukan da aka yi bayan taron koli na Beijing da taron ministoci a karo na uku. A gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin waje ta yi, malam Chen Jian ya gabatar da cewa, kasar Sin ta cimma burinta 'dan yawan taimakon da ta baiwa Afrika ya ninka sau daya, kuma yawan irin kayayyakin da ba za a buga harajin kwastan a kansu ba ya karu. Bugu da kari, an karasa aikin kawar da basussukan dake kan wasu kasashen Afrika. Dadin dadawa, an kaddamar da asusun raya Sin da Afrika. Ban da haka kuma, matasa da masu sa kai da kuma masana fasahar ayyukan gona na kasar Sin sun je Afrika bi da bi.

A shekarar bana, yawan kudin cinikayya a tsakanin Sin da Afrika ya kai dala 106.8, kuma yawan masana'antun kasar Sin dake taimakawa Afrika ya kai 1600.(Asabe)