Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 12:28:22    
Yankunan kudancin kasar Sin suna ci gaba da fama da fari

cri

Tun daga aka shiga yanayin kaka na bana, wasu yankunan tsakiyar kudancin kasar Sin kamar su lardunan Hunan da Anhui da Guangdong da dai sauransu suna fama da fari, hakan ya sa yawan ruwa da madatsan ruwa suka adana ya ragu sosai. Kawo yanzu dai, wurare da dama suna daukar matakai domin samar da isashen ruwan sha ga mazaunan kasa.

Saboda dalilin fari, yawan ruwa da madatsar ruwa da kogin Xiangjiang dake Changsha ta adana ya ragu har ya kai wani sabon matsayi a tarihi. Brinin Changsha babban birnin lardin Hunan ne ya dauki matakai a cikin gaggawa domin tabbatar da samun isashen ruwan sha.

Tun lokacin da lardin Guangdong ya shiga karancin ruwa a tsakiyar watan Octoba na bana, a kan fama da rashin ruwan sama. Yanzu, yawan amfanin gona da suke fama da fari a lardin Guangdong ya kai eka dubu 140, ban da wannan kuma, yawan mutanen da suke fama da karancin ruwan sha ya kai dubu 160. Saboda haka, lardin Guangdong ya zuba jari kamar miliyan 130 domin kawar da illar da fari ya jawo.

An habarta cewa, gwamantin kasar Sin tana zuba ido a kan lamarin. Hukumar dake jagoranci ga ayyukan yaki da bala'in ambaliyar ruwa da fari ta riga ta tura wata tawaga zuwa lardin Guangdong wanda ya fi fama da fari domin yin jagoranci ga ayyukan yaki da fari.(amina)